Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da soja tare da kashe guda 2 – NDA

Published

on

Kwalejin horas da sojojin Najeriya NDA ta tabbatar da farmakin da wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai.

NDA ta ce, harin yayi sanadiyyar mutuwar sojoji biyu tare da yin garkuwa da soja daya.

Wannan na cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na Kwalejin, Manjo Bashir Muhd ​​Jajira ya fitar.

Sanarwar ta ce, ƴan bindigar sun shiga cikin kwalejin a cikin abin hawan su, kuma suna sanye da kakin sojoji, inda kai tsaye suka wuce sssashin jami’an tsaro.

NDA ta kuma ce, za ta tabbatar da an ceto jami’in da suka sace nan ba da jimawa ba, tare da kamo ƴan bindigar.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!