Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kasuwanci

Ƴan kasuwa da mamallaka shagunan masallacin Idi sun yi Alkunutu

Published

on

Mamallaka shaguna da kuma masu yin kasuwanci a masallacin Idi da ke daura da Kasuwar Kantin Kwari a nan Kano, sun gudanar da Sallar Alƙunutu domin neman ɗauki Ubangiji bisa rushe shagunansu da suka ce gwamnati ta yi ba bisa ƙa’ida ba.

Ƴan kasuwar sun gudanar da Sallar ne da safiyar yau a tsakiyar masallacin inda suka gabatar da raka’a biyu tare da addu’o’i.

A ganawarsu da manema labarai, wasu cikin masu kasuwancin da kuma mamallaka shagunan, sun bayyana damu kan rushe wurin tare da cewa sun gina wurin ne bisa sahalewar gwamnatin baya, sai dai gwamnatin Engr. Abba Kabir Yusuf ta rushe musu shaguna ba tare da sanarwa ko umarnin kotu ba.

Malam Idris Bala Na Titi, guda ne cikin masu gudanar da kasuwanci a Kantinan da aka gina a masallacin, ya ce, ” Da misalin ƙarfe 1:30 na daren ranar 5 ga wannan watan da muke ciki ne gwamnatin jihar Kano ta fara rushe mana shaguna, hakan ta bai wa ɓarayi dama suka kwashe mana dukiya ta biliyoyin Naira,

Don haka muna kira ga gwamnati da ta waiwaye mu tare da biyan nasarar da aka janyo mana, An yi wannan ɓarna ne ba tare da sanar da mu domin mu kwashe kayanmu ba, kuma babu wani umarnin Kotu da aka samu gabanin wannan aika-aika.”

Shi kuwa Isiyaku Sani Isma’il, da ya mallaki shago a wurin ya bayyana cewa,” Mun mallaki wurin ne ta hannun masauta ta hanyar Abubakar Isah, shi ne wakilin masarautar Kano wajen sayar da wurin, shi ke shiga tsakani idan an bai wa jami’an gwamnati wurin kuma har yanzu babu wani bayani daga gwamnati a kanmu. Mu sayi wurin ne saboda mun ga ta hannun masarauta ake sayarwa”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!