Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan sanda sun kai sumame gidan Muhyi Magaji Rimin Gado

Published

on

Da tsakar daren ranar Lahadi ne jami’an ‘yan sanda suka durfafi gidan tsohon shugaban hukumar karbar korafi da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano Barista Muhyi Magaji Rimin Gado da nufin kama shi.

Jaridar Daily Nigerian ta rawaito cewa tun da karfe 7 na daren ne ‘yan sandan suka yi kwanton ɓauna a gidan Muhyi Magaji Rimin Gado da ke Yahaya Gusau, inda suka fara harbe-harben bindiga, kamar yadda wasu mazauna unguwar suka shaidawa Jaridar.

Sun kara da cewa da karfe 9:30 na daren ne dai suka ji alamar guje-gujen motoci kamar wani ya fito daga gidan da gudu an bi shi.

Ko da muka kira wayar Muhyi Rimin Gado ba ta shiga ba, kasancewarta a kashe.

Kan wannan ne wakiliyarmu Halima Wada Sinkin ta tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Kano Abdullahi Haruna Kiyawa, domin samun karin haske kan wannan yunkuri na kama Muhyi Magaji Rimin Gado, to sai dai ya ce yana cikin wata ganawa yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!