Labarai
Ƙofar mu A buɗe take wajen goyon bayan tsarin AGILE
Gwamnatin jihar Kano ta ce tsarin AGILE tsari ne da zai tallafawa ƴaƴa mata wajen samar musu da ilimi musamman a yankunan karkara.
Adan haka gwamnati zata ci gaba da bayar da gudummawa ga tsarin domin tsari ne da zai ƙara haɓɓaka harkar ilimin ƴaƴa mata.
Kwamishiniyar mata ƙananan yara da masu buƙata ta musamman Hajiya Aisha Lawan Saji ce ta bayyana hakan yayin wata ziyara da tawagar ta kawo ma’aikatar domin ƙara neman goyon bayan gwamnati musamman wannan ma’aikata ta Mata yara masu buƙata ta musamman.
Saji ta ƙara da cewa tana kira ga wannan tsari da zarar suna da wata buƙata ƙofar su a buɗe take wajen goyon bayan wannan tsarin.
Da yake jawabi Mataimakin shugaban tsarin AGILE Salisu Idris yace Wannan tsari ne haɗin gwiwa da babban bankin duniya domin tallafawa mata wajen samar musu da ilimi a yankunan karkara.
A dan haka wannan tsarin zai gina makarantu guda 130 na Firamare da sakandare da kuma gyara makarantun da suka sami matsala.
Yanzu haka akwai makarantu 1328 wa’inda suka anfana da wannan tsarin na gyara.
Akwai tsarin wayar da kai ga al’ummar gari domin fuskantar yadda tsarin na AGILE yake kan yadda ake bayar da tallafin karatun ga ƴaƴa mata musamman wajen basu kuɗin da zasu gudanar da karatun na su.
Haka kuma a cikin shirin akwai tsarin bayar da tallafi ga mata wajen gudanar da sana’o’i, ko da bayan sun kammala makarantar domin ci gaba da kasuwanci.
Wannan tsarin yafi mayar da hankali a yankin karkara sakamakon yadda ake samin katsewar karatun ƴaƴa mata a yankunan shiyasa tsarin yafi mayar da hankali a yankunan.
Haka zalika muna kira ga ma’aikatar Mata yara da masu buƙata ta musamman wajen ganin an bawa tsarin dama wajen shigewa gaba kan yadda za’a samarwa da ƴaƴa mata ilimi a yankunan karkara.
You must be logged in to post a comment Login