Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An sanya ranar zaben shugabanni da Kansiloli a Katsina

Published

on

Hukumar zabe a jihar Katsina ta sanya ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki a matsayin ranar da za a gudanar da zaben shugabanni da kansiloli a kananan hukumomin jihar.

Shugaban hukumar Alhaji Lawal Alhassan ne ya bayyaa hakan a ranar Laraba, lokacin da yake yiwa masu ruwa da tsaki jawabi kan shirin zaben.

Ya ce, an sanar da ranar zaben ne kamar yadda sashi na 197 na kundin tsarin mulkin kasa na 1999 ya bada dama.

Alhaji Lawal Alhassan ya kuma ce, duk dan takarar da yake sha’awar tsayawa a kowacce jam’iyya yana da damar yin hakan a zaben da ke tafe na shugabanni da kansiloli.

Ya kuma jaddada cewa, kowacce jam’iyya za a baiwa shugabanninta ka’idojin da aka tsara don yin biyayya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!