ilimi
Ƴan Najeriya su ba mu shawarar matakin da za mu ɗauka da ya fi yajin aiki – ASUU
Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU ta buƙaci ƴan Najeriya da bata shawarar matakin da ya kamata ta ɗauka a madadin yajin aikin da take tafiya wanda al’umma ke kokawa da shi.
Shugaban ƙungiyar mai kula da shiyyar Kano Farfesa Abdulƙadir Muhammad ne ya bayyana hakan ta cikin labaran Mu Leka Mu Gano na nan Freedom Radio da aka gabatar ranar Lahadi.
Ya ce, ƙungiyar ASUU ba ta da wani zaɓi da ya wuce shiga yajin aiki kamar yadda dokar ƙasa ta bada dama.
“Shekara 13 da muka ƙulla yarjejeniya da gwamnatin tarayya a 2009, da suka haɗar da yadda za a riƙa samun kuɗaɗen inganta jami’o’i da kuma batun albashi da alawus na ma’aikata, sai batun bai wa jami’o’i ƴancin cin gashin kai”.
Da yake amsa tambaya kan kalaman ministan ilimi Malam Adamu Adamu da ya bayyana cewa gwamnatin tarayya bata da masaniyar yajin aikin da kungiyar ASUU ta shiga, Farfesa Abdulkadir Muhammad ya c “lokaci yayi da ya kamata yan Najeriya su fahimci inda aka dosa, su san cewa shugabannin su basa son ci gaban su kuma ba inganta ilimin su ba ne a gaban su”.
Ya ci gaba da cewa “Ta yaya za a ce ministan ilimi guda ya ce bai san ASUU tana yajin aikin ba, ya kamata duba wannan batu domin mu ASUU ba ɓoyayyun mutane ba ne”.
Wannan dai na zuwa ne bayan da aka shafe mako guda da fara yajin aikin ƙungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU, da suka ƙuduri aniyar yi har na tsawon wata guda a matsayin gargaɗi.
You must be logged in to post a comment Login