Labarai
Ɓarayin dabbobi sun gurfana gaban kotu
Kotun majistire mai lamba 25 da fara sauraren wata shari’a da aka gurfanar da wasu matasa bisa zargin hada kai wajen satar dabbobi.
Kotun ƙarƙashin mai shari’a Halima Wali ta bai wa jami’in kotun Idris Sulaiman umarnin ya karanto musu tuhumar da ake yi musu, kuma nan take suka musanta sai dai guda daga cikinsu mai suna Abdullahi Nasir ya amsa laifin sata ba atre da ya hada kai da kowa ba.
Tun da fari dai an gurfanar da Abubakar Ibrahim (Gajiya) da wasu mutane 3 bisa tuhumarsu da hada kai wajen yin satar dabbobi, ta kwashe wasu dabbobi su kai su asibitin dabbobi da nufin cewa nasu ne suna zuwa asibitin sai su yi wa mai saye waya yazo ya tafi da su, wanda a nan ne aka same su da tumaki goma sha daya kuma aka kama su.
Lauyan gwamnati kuma mai gabatar da ƙara Barista Usaini Musa ya roƙi kotu da ta sanya wata ranar domin kawo shaida, sai dai Lauyan da yake kare Abdullahi Nasir, Barista A.A.Delmi ya roƙi a bashi belin wanda yake karewa.
Kotun ta amince bisa sharaɗin belin mutane biyu, wanda guda daga ciki mahaifinsa zai tsaya masa, ɗaya kuma mai unguwar mandawari kuma an bashi Naira dubu ɗari biyu idan ya gudu za’a kawo kotu.
Kutun ta ɗage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 7/3/2022 domin sake gabatar da su.
You must be logged in to post a comment Login