Labarai
NAFDAC ta kama jabun magunguna a Kano
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa, NAFDAC a nan Kano ta kai wani sumame karamar hukumar Bichi tare da kama wasu jabun magunguna da allurai na kimanin miliyan sha biyar.
Tun da fari dai wani mutum mai suna Muhammad Jamilu Sani Wanda ke hada magunguna da allurai na dabbobi a wani gida.
Shugaban hukumar Shaba Muhammad shi ne ya jagoranci sumamen ya bayyanawa wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail cewar sama da watanni 6 suna neman inda ake hada wannnan magani sai yanzu suka samu nasarar damke wannan mutum.
Shaba Muhammad ya kuma bayyana cewar zasu kai maganin da alluran dakin gwaji domin gano ko suna da illa ga lafiyar dabbobi, ya kuma ce cewar da zarar sun kammala bincike zasu gurfanar da jamilun a gaban kotu dan ya girbi abin da ya shuka
Shima Wanda aka zargin Muhammad jamilu ya bayyana cewar ya na da shaidar kammala karatu na babbar difiloma wanda yaje kwalejin Audu bako ya koyo ilimin harhada magungunan dabbobi.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya rawaito cewa tuni dai hukumar tayi awon gaba da magungunan da alluran don fadada bincike a kan su.
You must be logged in to post a comment Login