Labarai
2022: Za mu yaƙi bahaya a sarari – Dakta Getso
Gwamnatin jihar Kano ta ce, a shekarar 2022 za ta fi mayar da hankali wajen magance matsalar bahaya a sarari.
Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim Getso ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala duban tsaftar muhalli na kasuwanni ma’aikatun gwamnati.
Dakta Getso wanda ya samu wakilcin babban sakataren ma’aikatar Adamu Abdu Faragai ya ce, a bana an samu karin ƙananan hukumomi a jihar Kano da suka fita daga natsalar yin bahaya a sarari har guda 10.
Da yake batu kan nasarar da aka samu a tsaftar muhalli ya ce, “A shekarar 2021 ma’aikatar muhalli ta ziyarci ma’aikatu da hukumomin gwamnati talati 31”.
“Cikin ma’aikatu da hukumomin gwamnati da muka ziyarta 28 daga ciki sun samu yabo na tsaftar muhalli yayin da 3 daga ciki aka same su da rashin tsafta” a cewar Getso
Kwamishinan ya ce “Mun ziyarci mahauta guda 14 inda tara 9 suka bi umarnin gwamnati na tsaftar muhalli yayin da 5 suka saɓa doka kuma mun musu gyare-gyare”.
Har ma ya ce, jimillar tarar kudi da aka karɓa na waɗanda suka karya dokar tsaftar muhalli a bana ya kai naira miliyan biyar.
Dakta Kabiru Getso ya yabawa ƴan jarida bisa goyon bayan da suke bayarwa kan tafiyar da aikin, yana mai cewa ma’aikatar za ta ci gaba da hada kai da su wajen cimma manufofin da ake bukata.
You must be logged in to post a comment Login