Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Nan gaba kaɗan za mu dawo da Twitter – Buhari

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce nan gaba kadan za a dage dakatarwar da aka yiwa kamfanin kafar sada zumunta na Twitter.

Ministan yaɗa labarai da al’adu Alhaji Lai Muhammad, ne ya bayyana haka ga manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman majalisar zartarwar ta ƙasa.

Ministan ya ƙara da cewa tuni tattaunawa ta yi nisa tsakanin ɓangarorin biyu, wanda ba da dadewa ba za a cimma matsaya ta bai wa kamafnin damar dawo da ayyukan sa a fadin ƙasar.

A baya dai gwamnatin tarayya ta dakatar da kamfanin bisa goge kalaman shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da yayi tare da alaƙanta su da kalaman tayar da hankali da basu dace da tsarin kamfanin ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!