Labarai
NAHCON zata samo sabon kamfanin jigilar alhazai
Hukumar aikin hajji ta Nijeriya NAHCON ta kafa wani kwamiti da zai nemo wani sabon kamfanin da zai yi hidima ga alhazan kasar a lokacin aikin hajjin shekara mai zuwa ta 2024.
Shugaban hukumar NAHCON, Zikrullah Hassan, ne ya bayyana hakan a jiya alhamis yayin taron lakca da bada lambar yabo da aka shirya a Abuja.
A cewar Zikirullah, ana sa ran kwamitin da aka kafa zai samar da wasu hanyoyi da za a bi domin kyautatawa mahajjata kafin aikin hajjin shekara mai zuwa.
‘Haka zalika an raba guraben aikin hajji ga hukumomin jin dadin alhazai na jihohi domin fara shirye-shiryen aikin hajjin badi akan lokaci’.
A baya dai Alhazan kasar sun koka kan rashin yi musu hidima yadda ya kamata da wasu kamfanonin Saudiyya ke yi.
Rahoton: Abdulkadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login