Connect with us

Labarai

Gwamnatin Adamawa ta rushe rumfuna da shagunan da aka gina ba bisa ka’ida ba a kasuwar Jimeta

Published

on

Gwamnatin jihar Adamawa ta rushe rumfuna da shagunan da aka gina ba bisa ka’ida ba a cikin babbar kasuwar Jimeta da ke birnin Yola.

Wannan mataki ya biyo bayan umarnin da gwamnan jihar, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayar domin dawo da kasuwar yadda take a baya.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da aikin rushewar ne da nufin wanzar da tsari, da kawar da cunkoso da gina guraren kasuwanci ba tare da izini ba, wanda ke hana walwalar ’yan kasuwa da masu siyayya.

Gwamnatin ta ce za a ci gaba da irin wadannan matakan domin tabbatar da doka da oda a manyan kasuwanni da tituna a fadin jihar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!