Labarai
Gwamna Abba Kabir ya umarci shugabanin kananan hukumomin su samar da kwamitocin kula da Taransifoma

Gwamnatin Kano ta umarci shugabanin kananan hukumomin 44 na jihar da su samar da kwamitocin da zasu lura da saka naurorin Taransfoma guda dari biyar da gwamnatin ta samar.
Gwamna Abba Kabir Yusif, ne ya bayana hakan da yamacin ranar Lahadi a hukumar samar da lantarki a karkara ta jiha lokacin da ya ke kaddamar da rabon Taransifomomin.
Na’urorin guda 500 dai, gwamnatin jihar da kanana hukumomi ne suka yi hadin guiwa wajen samar da su.
Abba Kabir Yusif ya kara da cewar, samar da Taransifomomin zai taimaka wajen inganta rayuwar al’ummar jihar Kano da kuma bunkasa tatalin Arziki su.
You must be logged in to post a comment Login