Labarai

Babban Bankin kasar nan, CBN, ya sanar da cewa ƙasar nan ta samu rarar kuɗaɗen mu’amalar kasuwanci da ƙasashen waje da ya kai dala biliyan 4 da digo 60 a zango na uku a shekarar 2025 da mu ka yi bankwana da ita.
Rahoton da bankin ya fitar ya nuna cewa wannan ci gaba ya biyo bayan koma bayan da aka samu a zangon da ya gabata, inda aka danganta sauyin da karuwar ribar asusun kasuwanci na yanzu zuwa dala biliyan 3 da digo 42, tare da ƙarfuwar kuɗaɗen da ‘yan Najeriya ke turawa daga ƙasashen waje, da kuma ƙaruwa a harkokin kuɗi.
Ta cikin wata sanarwar da Hakima Sidi Ali, Darakta mai riƙon kwarya ta sashen sadarwar bangaren kamfanoni na Babban Bankin kasar nan ta fitar ta ce, wannan sakamako na zangon uku na 2025 na nuna ƙarfuwar tattalin arziƙin waje, da ƙarin kwarin gwiwar masu zuba jari, tare da tasirin gyare-gyaren da ake aiwatarwa a kasuwar musayar kuɗi da manufofin kuɗi.
You must be logged in to post a comment Login