Labaran Kano
‘Yan Fansho na jiran kudaden su a Kano
Shugaban kungiyar ‘yan fansho reshen jihar Kano Alh. Salisu Ahmed ya ce fiye da yan fansho dubu uku ke dakon karbar kudaden fanshon su da garatutin su na wadanda suka yi ritaya a shekara ta 2016 zuwa 2018.
Shugaban kungiyar ya bayyana haka ne a jiya yayin da ya jagoranci yan kungiyar fansho, kai ziyara ga shugaban majalisar jihar Kano Alh Abdulazeez Garba Gafasa.
Alh Salisu Ahmed ya kara da cewa fiye da yan fansho dubu 3000 ne da suka yi aiki karkashin gwamnatin Kano tun daga shekara ta 2016 2018 ne har yanzu basu karbi ko kobo ba daga hakokinsu na garatuti ba.
Hakan dai ya jefa da dama daga cikin yan fanshon cikin mawuyacin hali da kuncin rayuwa , yayin da wasu daga cikinsu tuni suka rasa rayukansu ba tare da sun karbi hakokinsu ba.
Shugaban ya kara da cewa ya zama wajibi ne su bayyana damuwarsu domin kuwa da dama daga cikinsu na fuskantar kuncin rayuwa, sakamakon rashin biyansu kudaden ritayar ta su.
Inda suka bukaci shugaban majlalisar jihar Alhaji Abdulazeez Gafasa da ya taimaka domin kawo musu karshen wannan matsala, tare da cewar sun yi aikinsu yadda ya kamata a yanzu lokaci ne da gwamnati itama zata ciki na ta aikin.
Tare da jan hankalin gwmamnati da ta sayar musu da gidajen da aka basu a wasu daga cikin jerin rukunin gidajen da gwamnati ta gina a wancan gwamnatin, domin kuwa manmobinsu wasunsu ba zasu iya sayan gida na naira miliyan 22 ba.
Shugaban kungiyar yan fanshon sun zargi ma’aikatar kananan hukumomi da hukumar bada ilimi na bai daya a matsayin wadanda suke kawo cikas sakamakon rashin bada nasu gudunmuwar ga ma’aikatan da suka yi aiki a karkashinsu ake cirar wani kasho daga kudadensu a yayin da suke aiki.
Shugaban majalisar ya bukuaci yan fanshon da gana da gwamna Abdullahi Ganduje domin nuna damuwarsu