Labarai
Rashin kwararru a bangaren ilimi ke kawo cikas – Tajudeen Gambo
Tsohon kwamishinan Ilimi na Jihar Kano Alhaji Tajudeen Gambo yace rashin kwararrun malamai da rashin kayayyakin koyo da koyarwa da kuma yadda iyake suka ta’allaka cewa lalle sai ‘ya’yan su sun sami shaidar kammala karatu shine ke ta’azzara matsalar magudin jarabawa a halin yanzu.
Alhaji Tajudeen Gambo ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Duniyar mu a yau na gidan Radio Freedom da ya maida hankali kan matsalar maguduin jarabawa a tsakanin dalibai a yanzu.
Tsohon kwamishinan Tajudeen ya kara da cewa matukar gwamnati da Iyaye da sauran al’umma basu dawo daga rakiyar mummunan tsarin da suke kai ba a yanzu yana mai cewa babu shakka al’umma zata cigaba da zama cikin hadari da tashin hankali, mudun ba’a dauki mataki ba.
Kano zata hada kafada da kasashen duniya a bangaren ilimi –Ganduje
Ya zama wajibi al’umma su baiwa ilimi fifiko-Dr Bashir Sani
Gwamnatin Kaduna zata baiwa daliban sakandire ilimi kyauta
Da yake nasa tsokacin shugaban Tsangayar Kula da jin dadin dalibai na jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano Dr. Yusuf Musa Kibiya cewa yayi dogaro da dalibai keyi dole sai sun sami shaidar kammala karatu kota halin kaka na daga abunda ke jawo matsalar.
Ana sa jawabin Dr.Misiwaru Bello na kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi cewa yayi tilastawa ‘ya’ya da iyaye keyi cewa dole sai sun karanta abunda iyayen su ke so koda kuwa ‘yayan na su ba su da ra’ayi na karantar fannin na daga abunda ke haddasa lamarin.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Tukuntawa ya ruwaito cewa dukkannin wadanda aka tattauna da su ta cikn shirin sunce matsawar gwamnati da iyaye basu fadawa kansu gaskiya ba wajen gyara wannan batu ba, tabbas haka al’umma zata cigaba da tafiya cikin matsala.