Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kyautatawa malamai ya zama wajibi- Shekarau

Published

on

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma Sanatan kano a yanzu Malam Ibrahim Shekarau yace matukar anaso harkar Ilimi ta gyaru a fadin kasar nan ya zama wajibi Gwamnatocin jihohi su dauki gabarar gyara tsarin yadda Gwamnati ke daukar Malaman Makarantu.

Malam Ibrahim Shekarau wanda ya sami wakilcin Ahmad S Aruwa ya bayyana hakan ne lokacin bikin cikar kungiyar tsaffin daliban Kabo Old Girls Association KOGA aji na tamanin da tara shekara talatin da kafuwa.

Ahmad S Aruwa ya kara da cewa akwai bukatar tsaffin kungiyoyin Dalibai su rika kokarin kyautatawa Malaman da suka koyarda dasu domin ta sanadiyyar Malaman ne daliban suka zama wasu.

Rashin kwararru a bangaren ilimi ke kawo cikas – Tajudeen Gambo

Akwai karancin ilimin harkar fim ga masu shirya fina-finai

Kano zata hada kafada da kasashen duniya a bangaren ilimi –Ganduje

Alhaji Ahmad S Aruwa ya kuma shawarci sauran tsaffin daliban Makarantu dasuyi koyi da irin kokarin da kungiyar ke yi musamman wajen taimako da sada zumunci.

Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito an gudanar da makaloli dake nuni da muhimmancin zumunci kamar yadda yake a cikin addinin Musulunci.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!