Labarai
Lauyoyi sun nemi majalisar Kano ta jingine batun dokar kafa masarautu 4
Wani ofishin lauyoyi a nan Kano ya bukaci gwanan Kano da majalisar dokoki da su jingine batun sake gyaran dokar kafa rusassun masarautun Bichi, Karaye, Gaya, da Rano, wanda mai shari’a Usman Na abba na babbar kotun jIha ya rushe makonni biyu da suka gobata .
Ofishin lauyoyin da suke wakiltar madakin Kano da mutum uku a kunshin Sharia mai lamba K/ 197/2019 wadda take gaban babbar kotun jiha mai lamba uku karkashin Justice Ahmad Tijjani
Har ila yau, Cikin wadanda ake kara a wannan Sharia Sun hadar da shugaban majalisa da Baturen Sharia da gwamnatin Kano da kuma babban Baturen Sharia.
Haka zalika wakilin mu Yusuf Nadabo Isama’il ya rawaito cewa, ofishin lauyoyin Sun bukaci a jingine wannan batu na gyaran dokar kirkirar masarautu tun da dai maganar da take gaban kotu kowa tsayawa yake ya jira hukuncin kotun ba batun gaban kai gaba.
Ina rokon Ganduje ya rushe shirinsa na rarraba masarauta -Sheikh Dahiru Bauchi
Gwamnatin Kano ta amince da dokar dawo da masarautu hudu
Gwmantin Kano ta musanta yunkurin sauya wa sarkin Kano Masarauta
Sai dai a dazu ne majalisar dokokin jihar Kano ta gaza cimma matsaya a yau laraba game da kirkiro masarautun gargajiya
kudirin dokar kirkiro da sababbin masarautu guda hudu a jhar Kano Bayan kwashe kusan awanni uku mambobi na zaman sirn kan kudirn dokar, sun fito daga zaman ba tare da d gaba da zama domin daukar mataki kan kudirin dkar ba.
Majalisar ta kuma dage d gaba da zama zuwa gobe Alhams wancia 8 l’adance ba rana ce da majalisar ta saba zama ba.
Tun farko sai da mambobin majalisar su ka dau tsawon lokad suna muhawara kan kudinin dokar, kafin daga bisani shugaban masu rinjaye na majalisar Abdul Labaran Madarl, ya nemi da majalisar ta shiga zaman sirn
domin tattauna kudirin da kuma kudirin dokar hukumar bunkasa harkokin
ilimi.
Wakilin mu na majalisar dokokin jihar Kano Abdullahi 1sah ya ruwaito cewa, ana saran majalisar za ta zauna gobe domin cigaba da tattauna kan batun.