Labarai
Muna fuskantar kalubale – masu bukata ta musamman
Masu bukata ta musamman suna fuskantar tarin kalubale acikin al’umma wanda hakan ya sa suka samarwa kansu doka a jihar Kano.
Shugaban kungiyar masu bukata ta musamman Abba Sarki yace sun samar da doka da aka sa mata hannu wacce ta hada da samarwa masu bukata ta musamman hanyoyi domin su samu saukin zirga zirga.
Ana sa bangaren Sakataren kungiyar Mukhtar Ilyasu Dumbulun yayi kira ga gwamnati kan cewa masu bukata ta musamman suna da tarin matsaloli na rayuwa ba iya hanyace matsalarsu kawai ba, wanda ya kamata gwamnati ta duba kuma ta bunkasa rayuwarsu a cikin al’umma.
Masu bukata ta mussaman sun sami tallafi -Dr. Bunkure
INEC: ta bijiro da salon tsari na baiwa masu bukata ta mussaman damar zabe
Kungiyar dalibai ta Najeriya ta bukaci a rika gina makarantun masu bukata ta musamman
Masu bukata ta musamman a Kano sun shirya taro gabanin ranar bikin ta masu bukata ta musamman inda gwamnatin jihar Kano ta sha alwashin cigaba da tallafa musu domin su cimma muradansu na rayuwa.