Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Ana zargin KAROTA da haddasa hatsari a titin Zariya

Published

on

Daga Shamsu Dau Abdullahi

Wani hadari mota daya auku a safiyar yau akan titin Zaria Road a nan Kano ya haddasa asarar dukiyoyi da dama baya ga janyo cunkoson ababen hawa wanda ake zargin jami’an hukumar kula da zirga zirga ababen hawa ta jihar kano Karota ne suka yi sanadiyar faruwar al’amarin.

Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa hadarin ya auku ne da misalin daya na daren jiya inda wata mota kirar J5 dauke da goro tayi awon gaba da wata tirela bayan da jami’an hukumar Karota suka tsayar da ita domin bincikarta.

Sun kuma ce ba’a samu asarar rayuka ba sai dai a sarar dukiyoyi mai tarin yawa wanda ya tunzura direbobin tirelan suka rufe hanyar ba shiga ba fita akan titin.

Mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon kazamin hatsarin mota a Kano

Takai:Mutane 19 ne suka rasa rayukansu a wani hatsari da ya afku a kauyen Dinyar Madiga

Ko da muka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar Karota Nabilisi Abubakar Kofar  Na’isa ya tabbatar da faruwar al’amarin yana mai cewa a yanzu haka tuni hukumar ta fara bincike don daukan mataki na gaba akan jami’an da ake zargin su.

A nasa bangaren shugaban hukumar kare aukuwar hadari ta kasa reshen jihar kano Zubairu Mato cewa yayi sun sami wannan labari ne da safiyar yau shiyasa suka tura jami’ansu domin kawo daidaito akan titin.

 

Shugaban hukumar yayi kira da direbobi dasu daina tuki wanda ya wuce sa’a a cikin gari dama wajen gari.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!