Kiwon Lafiya
Mambobin kungiyar JUPTI sun tsunduma yajin aiki bisa rashin albashin watanni 5
Hadaddiyar kungiyar malaman manyan makarantu ta jihar Plateau JUPTI ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani saboda rashin biyan albashin malamai na watanni biyar.
Rahotanni sun bayyana cewar, kungiyar ta dauki wannan matakin ne biyo bayan wata wasika da uwar kungiyar ta aikewa gwamna jihar mai kwana wata 23 ga watan jiya dake dauke da sa hannun hadin gwiwa na shugaban Mr Paul Dakogol da kuma sakataren ta Ayum Solomon suka sanya wa hannu.
Amma kuma a karshen shekara ta 2016, gwamnatin jihar ta yi alkawarin zata biya malaman dukkanin hakokin su.
Haka zalika rahotanni sun bayyana cewar, an hana dalibai shiga harabar kwalejin kimiya da fasaha ta jihar da sauran manyan makarantu, saboda matakin da kungiyar ta dauka da tsunduma yajin aiki.