Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A gaggauce: Buhari ya aike da tawaga ta musamman zuwa jihohin Sokoto da Katsina

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya aike da wata babbar tawaga wadda ta ƙunshi shugabannin hukumar Leƙen asiri da tsaro ta ƙasa zuwa jihohin Sokoto da Katsina, sakamakon karuwar ayyukan ta’addanci a Jihohin.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce, tawagar da shugaba Buhari ya tura yana sa rai su kawo masa rahoton halin da ake ciki cikin gaggawa da kuma shawarwari kan hanyoyin da za a bi don tinkarar lamarin.

Tawagar na ƙarƙashin jagorancin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Munguno mai ritaya ta ƙunshi babban sufeton ƴan sanda, Usman Alkali Baba da babban darakta janar na ma’aikatar harkokin waje, Yusuf Magaji Bichi.

Sai darakta janar na hukumar Leƙen Asiri ta ƙasa, Ambasada Ahmed Rufa’i Abubakar da shugaban hukumar Leken Asiri da tsaro, Manjo Janar Samuel Adebayo.

Ko a ranar Alhamis sai da shugaba Buhari ya bayar da umarnin a nemi waɗanda suka yi kisan gilla ga kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Jihar Katsina, Dr Rabe Nasir.

Kwanaki kaɗan bayan wani hari da ƴan bindiga suka kai kan matafiya daga Sokoto zuwa jihar Kaduna wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 23.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!