Connect with us

Labarai

A na sa ran Ministan harkokin kasashen waje zai gana da shugaban hukumar INEC a yau

Published

on

A yau ne ake saran ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama, da shugbaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, Ferfesa Mamudu Yakubu, zai gana da jakadojin kasashen waje da ke kasar nan.

Rahotanni sun ce taron zai mayar da hankali ne kan batun dage zaben da hukumar ta INEC ta yi a baya-bayan nan.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen wajen kasar nan mista Gearge Edokpa ne bayyana hakan, yayin zantawa da manema labarai a birnin tarraya Abuja.

A cewar sa, Geofrey Onyeama da shugaban hukumar ta INEC Farfesa Mahmud Yakubu za su gabatar da mukaloli dangane da dalilan da suka sanya aka dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun dokokin tarraya. 

Ana kuma sa ran za a fara taron ne da safiyar nan, a  ma’aikatar kasashen waje da ke birnin tarraya Abuja.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,480 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!