Labarai
Abin da ziyarar Tinubu zuwa Dubai ta kunsa

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya dawo Najeriya bayan halartar taron Abu Dhabi Sustainability Week na shekarar 2026, wanda aka gudanar a birnin Abu Dhabi na Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
A yayin taron, Shugaba Tinubu ya halarci zaman tattaunawa da shugabannin ƙasashe da manyan jami’an ƙungiyoyi na duniya, inda aka tattauna batutuwa da suka shafi ci gaba mai ɗorewa, makamashi, sauyin yanayi da kuma hanyoyin bunƙasa tattalin arziki.
Rahotanni sun ce ziyarar ta Shugaban Ƙasa na da nufin ƙarfafa alaƙar Nijeriya da ƙasashen duniya, tare da jawo hankalin masu zuba jari a fannonin makamashi da cigaba mai ɗorewa.
You must be logged in to post a comment Login