Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abin takaici ne yadda Iyaye ke watsi da Ilimin Yayan su – Wazirin Dutse

Published

on

Wazirin Dutse Alhaji Bashir Dalhatu ya ce, dole sai Iyaye sun taimakawa Ilimin Yayan su idan har ana san samun ci gaban Ilimi yadda ya kamata a jihar Kano dama yankin Arewawacin Najeriya.

Alhaji Bashir Dalhatu Kuma shugaban kwamatin amintattun na kungiyar Dattawan Arewa (ACF) ne ya bayyana hakan jim kadan bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban amintattun kungiyar tsofaffun Daliban makarantar Yan Mata ta shekara dake Kano.

Taron an gudanar dashi ne a ranar Talata 24 ga watan Disambar shekarar 2024.

Alhaji Bashir Dalhatu yayin taron ya kuma ce abin takaici ne yadda Iyaye ke haifar Yaya suna zubar da su ba tare da sun Kula da rayuwar su ba musamman Ilimi yadda ya kamata a wannan lokaci.

Ya Kuma ce, a kididigar da aka samu da yawa daga cikin Yaya Mata basa zuwa makaranta sakamakon sakacin Iyaye da suke nuna halin ko in Kula da karatun su.

Ya Kuma ce Babu wata mafita da al’ummar Arewacin Najeriya ta rage musu sama da Kula da Ilimin Yayan su.

Da ta ke jawabi yayin Taron Farfesa Binta Tijjani Jibril Malama a Jami’ar Bayero dake jihar Kano Kuma tsohuwar daliba a makarantar ta Shekara da ta gabatar da Lakcha kan muhimmancin neman Ilimin Yaya Mata Cewa ta yi, “ya kamata tsofaffun Dalibai su bayar da gudunmawar data kamata wajen ciyar da Ilimin Yayan su musamman Mata”.

A na ta jawabin shugabar kungiyar tsofaffun Daliban makarantar Yan matan ta Shekara wato Shoga Barrister Amina Ummulkhar Ibrahim BB Faruk Cewa ta yi, abin takaicine yadda ake barin wasu makarantun na Lalacewa, ta Kuma ce “Mu ne zamu gyara makarantun mu Dan Yayan mu su Samu Ilimi Mai amfani”.

Taron ya samu halartar babban sakatare a ma’aikatar ta jihar Kano da shugabannin makarantar ta Shekara Dana masarautun gargajiya da dai sauran su.

An kuma karrama wasu dake bayar da gudunmawar wajen ciyar da Ilimi gaba.

Haka Kuma kungiyar tsofaffun Daliban makarantar ta Shekara ta ce a bana ta zakulo shugabannin kowacce shekara wato Chapter na tsofaffun Dalibanta domin tattauna yadda za a ciyar da makarantar gaba tsawon shekaru 64 da kafata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!