Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

Abinda yasa ‘yansanda suka cafke Sadiya Haruna

Published

on

Rundunar ‘yansanda ta jihar Kano ta tabbatar da kame Sadiya Haruna shahararriyar jarumar nan ta soshiyal midiya.

Kakakin rundunar ‘yansanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatarwa da Freedom Radio cewa ‘yansanda na tsare da Sadiyan sakamakon korafin da jarumin fina-finan Hausa Isa I. Isa yayi, na zargin taci zarafinsa da kuma bata masa suna.


DSP. Kiyawa ya kara da cewa suna cigaba da bincike akai domin gurfanar da wanda aka samu da laifi a gaban kotu.

Tun da farko dai Sadiya Haruna ta fitar da wasu bidiyo ta dandalin sada zumunta na Instagram inda ta kalubalanci jarumin Isa I. Isa da aikata wasu laifuka.

Sai dai jarumin ya fitar da wani bidiyo da ya nemi afuwar jama’a, kan wani laifi da yayi ikrarin ya aikata, amma daga baya ya goge shi.

Haka ma dai ita ma Sadiyan izuwa yanzu ta goge bayanan da ta wallafa a shafin nata game da Isan.

Allah ya kyauta.

Rubutu masu alaka:

Yadda akayi auren mutu’a a Kannywood

mKun san abinda ya hana jaruma Maryam Yahya aure?

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!