Labarai
Abubuwan da Ɗan China yayi iƙrarin ya kashewa Ummita
Ɗan ƙasar Chinan nan Mr. Frank Geng ya yi iƙirarin kashe wa marigayiya Ummita maƙudan kudade.
Ɗan sanda mai binciken lamarin Ijuptil Mbambu ne ya bayyana hakan a gaban Kotu.
Ya ce, yayin da suke bincike Geng ya shaida musu cewar ya turawa marigayiyar Naira miliyan Sha takwas a matsayin jari.
Sannan ya siya mata Gida na Naira Miliyan hudu.
Bayan kammala ba da shaidar ɗan sandan mai shari’a Sunusi Ado Ma’aji ya dage Shari’ar zuwa Ranar 19 da 20 da kuma 21 na watan Disamba domin ci gaba da shari’ar.
You must be logged in to post a comment Login