Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abun takaici ne mawadata basa tallafawa dalibai-Dr, Nafi’u Dan-nono

Published

on

Wani mai hannu da shuni Dr. Nafi’u Yakubu Dan-Nono da ke karamar hukumar Tofa, ya bayyana takaicin sa dangane da yadda masu hali basa tallafawa dalibai kan harkokin karatun su.

Dr. Nafi’u Yakubu ya bayyana hakan ne lokacin da yake rabawa wasu daliban tallafin kudi Naira Dubu goma-goma ga daliban kwaleji sai Naira duba Ashirin-Ashirin ga daliban jami’a, a jiya Lahadi a karamar hukumar Tofa, a wani bangare na taimakawa daliban ‘yan asalin karamar hukumar Tofa.

Dr Nafi’u ya kara, ya bada tallafin ne sakamakon yawan samun koken daliban  kan ya taimaka musu.

A cewar Dr, Nafi’u ya zama wajibi a taimaka wa daliban ganin cewa ilimi shi ne kashin bayan kowacce al’umma

Wasu dalibai da suka ci gajiyar tallafin sun bayyana jin dadin su tare da yin godiya ga Allah ma daukakin sarki, saboda samun wannan tallafin.

Dalibai fiye da dari uku sun sami tallafin karatu-Sha’aban

An zargi shugabar makaranta da amsar kudin dalibai

Da gaske Adam Zango ya dauki nauyin karatun dalibai?

Wakilin mu Umar Lawan Tofa ya rawaito mana cewa, kimanin dalibai dari biyu ne daga makarantun gaba da sakandire daban-daban ne suka amfana.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!