Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalibai fiye da dari uku sun sami tallafin karatu-Sha’aban

Published

on

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar birni da kewaye a majalisar wakilai kuma shugaban kwamitin kula da al’amuran tsaro na majalisar Sha’aban Ibrahim Sharida ya ce ya dauki nauyin dalibai fiye da dari da zasu je kasashen wajen don karu karatu.

Sha’aban Ibrahim ya bayyan hakan a cikin shirin barka da hantsi na nan tashar Freedom Radio wanda ya mai da hankali kan yadda yake gudanar da ayyukan sa bayan ya kama aiki a matsayin sa na shugaban kwamitin tsaro.

Dan majalisar ya ce a halin yanzu an kammala komai na dalibai fiye da saba’in wanda za su bar gida Najeriya don zuwa kasashen wajen don yin nazari a bangarori daban-daban na ilimi.

Haka zalika Sha’aban Ibrahim a gefe guda ya ce  kwamitin sa na kokarin inganta tsaro a sassan kasar nan yana mai cewa a shirye  yake ya kawo karshen ‘yan ta’adda da ayyukan bata gari da suka addabi kasar nan.

Muna rokon gwamna Ganduje ya sulhunta Muntari da Sha’aban –Habib Sadam

Tsofaffin dalibai: Za mu tallafa wa jami’ar Bayero

Da yake magana akan batun ceto yara tara ‘yan asalin jihar Kano da aka sace aka saida su a jihar Anambra, dan majalisar ya ce nan bada jimawa kwamitin tsaro na majalisar zai kawo karshen yin garkuwa da mutane da kuma sace-sace yara da ake fuskanta a Arewacin kasar nan.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!