Connect with us

Kiwon Lafiya

Adamawa:Al’ummar karamar hukumar Madagali na cikin dar-dar

Published

on

Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa yanzu haka dai al’ummar kauyen Pallam da ke yankin karamar hukumar Madagali na cikin dar-dar sakamakon harin da kungiyar Boko Haram ke kaiwa, tare da garkuwa da wasu mutanen yankin.

Harin na zuwa ne, a dai-dai lokacin da mutanen ke tsaka da jimamin rashin yan uwan su, sakamakon harin da kungiyar ta Boko Haram ta kai kauyukan da ke makwatbataka da su, da suka hadar da Wanu, Kamale, Kafin Hausa da Minchika da kuma Madagalin.

Wasu daga cikin al’ummar da ke yankin sun bayyana cewa kalalla awanni biyar mayakan na Boko Haram suka dauka suna kaddamar musu da hari, wanda kuma hakan ya sanya wasu ficewa daga kauyukan domin tseratar da lafiyar su.

A cewar mazauna yankin Pallam mayakan sun shiga kauyen ne da tsakar dare, inda suka fara kaddamar da harbi, tare da kashe mutane da kuma kona musu gidaje, inda daga bisani kuma sukayi garkuwa da wasu.

Rundunar yan sandan jihar ta bakin kakakin taOthman Abubakar ta tabbatar da faruwar wannan al’amari.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,676 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!