Connect with us

Kiwon Lafiya

Kungiyar RANAO ta bukaci a rushe uwar kungiyar tsofaffin sojoji ta Nigerian Legion

Published

on

Kungiyar tsofaffin sojoji ta RANAO ta bukaci a rushe uwar kungiyar tsofaffin sojoji ta Nigerian Legion da kuma kafa wata hukumar da za ta rika kula da al’amuran mazan jiya a kasar nan.

Jami’in yada labaran kungiyar reshen jihar Kano Kyaftin Yusuf Abdulmalik mai ritaya ne ya yi wannan kiran da safiyar yau, yayin zantawarsa da gidan rediyo freedom.

Ya ce tsawon lokaci tsofaffin sojoji a kasar nan na fama da rashin kulawar hukumomi sakamakon rashin iya shugabanci na jagororin kungiyar ta Legion, a cewar sa ranar mazan jiya ba ta da wata daraja a wajensu a yanzu sakamakon mawuyacin hali da suke ciki.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,961 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!