Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ahmed Musa zai dauki nauyin karatun dalibai 100 a jami’a

Published

on

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Ahmed Musa ya bayyana cewa zai dauki nauyin karatun dalibai 100 a jami’ar Skyline dake Kano.

Ahmed Musa ya bayyana hakan ne bayan jami’ar ta nada shi a matsayin jakadanta sakamakon irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban matasa ta hanyar bunkasa ilimi da harkokin wasanni a arewaci, dama Nigeria baki daya.

Ya ce duba da muhimmancin da ilimi yake da shi ga ci gaban ko wace al’umma ya ga akwai bukatar kulla alaka tsakaninsa da jami’ar domin tallafawa matasa da guraben karatu.

 

Ahmed Musa wanda ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr dake kasar Saudiya ya godewa jami’ar bisa wannan matsayi da ta ba shi, inda yayi alkawarin bawar da duk gudunmawar da ta dace wajen bunkasa harkokin ilimi.

Kyaftin Ahmed Musa ya taka rawar gani a wasanni biyu da Najeriya ta buga da Jamhuriyar Benin da Lesotho a wasannin naiman cancantar zuwa gasar cikin kofin Afrika na shekarar 2021 wanda kasar Cameroon zata karbi bakunci.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!