Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Aisha Bahari ta soki shirrin Gwamnatin tarayya na rage fatara

Published

on

Mai dakin shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari, ta ce, shirin gwamnatin tarayya na rage fatara da samar da aikin yi ga matasa  bai samu nasara ba a yankin arewacin kasar nan.

Uwargidan shugaban kasar ta bayyana hakan ne lokacin da ta ke tattaunawa da mata a fadar Asorok da ke Abuja a jiya Asanar.

A cewar uwargidan shugaban kasar akwai lokacin da ta samu daya daga cikin jagorororin da ke kula da shirin wanda ya tabbatar da mata cewa mata dubu talatin za su amfana da shirin bai wa mata dubu goma-goma a jihar ta, ta Adamawa amma har ya zuwa yanzu babu amo ba labari.

Mai dakin shugaban kasar ta ma buga misali da wani dattijo maishekaru saba’in da hudu da ta ce ta ganshi a gefen titi a Kano, yana sayar da kayayyaki da ta tambaye shi ko nawane jarin sa ya ce bai wuce dubu uku zuwa hudu ba lamarin da ke nuna cewa da an bashi dubu goma zai bunkasa kasuwancin sa.

Jawabin nata na zuwa ne kwanaki uku bayan da mai bai wa shugaban kasa shawara kan shirin samar da aikin yi Maryam Uwais ke cewa gwamnatin ta kashe sama da naira biliyan dari hudu da saba’in tun farkon fara shirin.

Shirin yaki da fatara da samar da aikin yi ga matasa sun hada da: Shirin Npower da shirin ciyar da daliban makarantun firamare da shirin ba da kudade ga kananan ‘yan kasuwa da sauransu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!