Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Bahari ya soki Shugabannin dokokin tarayya

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana Shugabannin majalisun dokokin tarayya Sanata Bukola Saraki da Yakubu Dogara a matsayin wadanda ke da karancin kishin kasa.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke hira ta musamman da gidan talabijin na NTA a daren jiya.

A cewar shugaba Buhari ko kadan bai ji dadin halayyar Shugabannin majalisun biyu ba sakamakon yadda suka rike kasafin kudin bana a wajen su har na tsawon watanni bakwai saboda kawai bukatun kashin kansu.

Haka zalika shugaban kasar ya kuma ce rundunar ‘yan sandan Najeriya da Shugabannin al’umma sun gaza matuka wajen gudanar da hakkokin da ya rataya a wutar su.

Sai dai ya ce yana fata ‘yan sanda da bangaren shari’a za su kara zage dantse wajen aiwatar da hakkokin da ya rataya a wuyar su a zangon mulkin sa na biyu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!