Labarai
Akpabio ya musanta cewa ya na fama da rashin lafiya

Shugaban majalisar dattawa Sanata Godswill Akpabio ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa na cewa yana fama da rashin lafiya.
Akpabio ya bayyana hakan ne a lokacin da ya sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yau Litinin bayan ya dawo daga birnin London.
Da ya ke jawabi ga manema labarai a filin jirgin, Akpabio ya ce, batun rashin lafiyarsa labari ne mara tushe ballantana maka
Kafin zuwansa London, Akpabio ya halarci taron shugabannin majalisa na ƙasashen duniya da aka yi a birnin Geneva na ƙasar Switzerland daga ranar 29 ga watan Yuli zuwa 31.
You must be logged in to post a comment Login