Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Akwai yiwuwar dawo da kuɗin tsaba a Najeriya

Published

on

Majalisar wakilai ta buƙaci babban bankin ƙasa CBN daya tilasta yin amfani da kuɗaɗen tsaba a Najeriya.

A cewar majalisar yin hakan zai kawo ƙarshen matsalar hauhawan farashin da ake fuskanta na kayan masarufi kuma zai kawo daidaituwar tattalin arziƙi.

Wannan dai ya biyo bayan ƙudurin da ɗan majalisa mai wakiltar Toro ta jihar Bauchi Umar Lawal ya gabatar a zaman majalisar.

Ƙudirin ya kuma buƙaci babban bankin ƙasa CBN ya sanya dokar yin amfani da kudaɗen na tsaba domin farfaɗo da tattalin arziƙi.

Har ma yayi ƙorafin cewa a Najeriya an jima dayin watsi da amfani da kudaɗen tsaba wanda hakan ya haifar da koma baya a tatalin arziƙi da ake gani a yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!