Labarai
Akwai yiwuwar zan fafata da Tinubu a zaɓen 2027- Rotimi Amaechi

Tsohon ministan sufuri a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi, ya ce akwai yiwuwar zai fafata da Shugaba Tinubu a zaɓen shekarar 2027.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa tsohon gwamnan na jihar Rivers ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi, a baya bayan nan.
Amaechi, wanda ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC wanda ya samar da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a 2022, ya ce bai cire yiwuwar tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027 ba, yana mai cewa lokaci ne zai nuna hakan.
Bayanin nasa na zuwa ne ƙasa da wata guda bayan shugabannin APC sun amince da Tinubu a matsayin ɗan takara guda ɗaya na jam’iyyar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Shugabannin adawa da suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, kana tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da wasu da dama, suna ƙoƙarin kafa haɗaka don ganin sun kayar da Tinubu a zaben 2027.
You must be logged in to post a comment Login