Rahotonni
Al’adar “Ciyayya” na neman zama tarihi
Al’adar nan ta iyaye da kakanni wato “Ciyayya” a yanzu na neman zama tarihi a tsakanin mutane a wannan zamani, sai dai abun tambayar shine shin ko menene ya jawo hakan?
Shekaru aru – aru da suka gabata a kasar Hausa, al’ummar Hausawa sunyi kaurin suna akan al’adar Ciyayya wanda kusan kowanne gida a lokacin da zarar an kammala sallar Isha zaka iske magidanta sun fito da abinci waje an kewaye shi ana kwasar girki.
Sai dai ana alakanta al’adar ta Ciyayya wanda a yanzu ke tasamma zama tarihi da cewa hanyace tilo dake sanya kaunar juna da hadin kai a tsakanin makota sabanin yadda a yanzu ake samun rashin jituwa a zaman makotaka.
Labarai masu alaka:
Wani Sabon gidan abincin Naira Talatin ya hana wasu Almajirai bara a Kano.
Kungiyar Rumbun abinci na taimakawa yara masu tamowa da abincin gina jiki a Kano
Wasu dai na kallon Ciyayya da iyaye da kakanni keyi a baya a matsayin al’ada ce kawai, wanda kuma a yanzu wasu suka alakanta daina yin Ciyayya da matsin tattalin arziki da mutane ke fama dashi ba kamar yadda abin yake ba a baya.
To koma dai menene ya janyo hakan, wani Malamin addinin misulunci a nan Kano Malam Nuhu Muhammad a tattanawarsa da wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa yace al’adar Ciyayya abune mai kyau kuma ta samo asali ne daga wajen Annabi (s.a.w), kamar yadda kowa ya sani Annabi da dabi’ar tara Sahabbai waje guda musamman marasa karfi su ci su sha saboda muhimmincin da ciyarwa ke dashi a musulunci.
Shehin Malamin ya kara da cewa da ace mutane sun cigaba da dabbaka al’adar Ciyayya a yanzu ko kadan ba za’a rika samun tashin hankali ba tsakanin makoci da makoci wanda wani lokacin matsalar kanyi kamari takai har wajen ‘yan sanda ko Kotu.