Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Rahotonni

Muhimman abubuwan da sarkin Kano yayi a gwamnan banki

Published

on

A irin wannan rana ta 20 ga watan Fabrairu na shekara ta 2014 tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya dakatar da gwamnan babban bankin kasar Sanusi Lamidu Sanusi daga mukaminsa na Gwamnan CBN.

Hakan ya biyo bayan da ya bankado wata badakalar rashin sanya kudin sanya kudaden haraji a asusun gwamnati na kamfanin NNPC kimanin dala biliyan Ashirin da Sanusi Lamido ya a wancan lokaci.

Duk da cewa a watan Yuni na shekarar ta 2014 ne Sanusi Lamido zai kammala wa’adin mulkinsa a babban bankin, sai dai a wata tattaunawa da yayi da BBC Hausa a wancan lokacin ya bayyana cewa tun a watan Janairu na shekarar shugaban kasa a wancan lokacin Goodluck Jonathan ya nemi da ya ajiye mukaminsa.

Hoton tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Sarkin Kano Mallam Muhammadu Sanusi II.

Freedom Radio ta nazarci wasu daga cikin ayyukan da Sarki Muhammadu Sanusi II ya gudanar a lokacin da yake rike da mukamin gwamnan babban bankin kasar nan.

A shekara ta 2012 ne Sanusi Lamido Sanusi ya kaddamar da tsarin takaita ta’ammali da kudade a hannun jama’a wato Cashless Policy wanda tsarin ya kunshi bangarori da dama wadanda suka hada:-

ATM: Al’ummar Najeriya sun ta tafka muhawara a wancan lokacin tsakanin wadanda suke ganin tsarin ATM ba zai yiwu ba a Najeriya, da kuma wadanda suke ganin cewa tsarin zai yiwu, mafi yawan jama’a a wancan lokaci na korafin cewa ina ma aka samu tsayayyen Network da za’a iya yin na’urar cirar kudi ATM?

Mobile Banking: Tsarin amfani da wayoyin hannu ta hanyar sarrafa kudi wajen aikawa ko karba kudi wato Transfer.

SMS Alert: tsarin samun sako idan an turo maka kudi, ko an ciri kudin ka ta wayar hannu.

Al’amarin ya kara bunkasa domin kuwa kowane banki suna da tsarin amfani da bankinsu ta hanyar danna lambobi wanda ake yiwa lakabi da USSD Banking, sannan kowane banki ya mallaki manhaja da mai amfani da ita zai iya ganin me yake dashi a asusun sa, nawa ne ya fita, cirar rasiti, da biyan kudaden hukumomi da sauransu.

A yayin da yake rike da mukamin Gwamnan babban bankin kasa ya samar da bankin musulunci na Ja’iz wanda babu tsarin kudin ruwa a cikin sa

batun ya tada hazo kasancewar wasu na yi wa kafa bankin kallon bai dace ba.

Labarai masu alaka:

Matsalolin aure: Sarkin Kano ya bukaci a koma makaranta

Sarkin Kano ya ankarar da jama’a kan cutar Lassa

Internet Banking: Baya ga amfani da mahajoji na wayar hannu, a wannan lokaci ne kuma Sanusi Lamido ya hada da tsarin sarrafa kudi a banki ta internet.

Bank Verification Number (BVN): Bayan da gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da lambar tantacewa a banki, hakan ya sanya an bankado asusu da dama da ake zargi da satar kudaden talakawa, daga ciki akwai asusun matar tsohon shugaban kasa Jonathan wanda ake zargin ta bude da sunan ‘yar aikin ta.

Sannan wannan tsarin ne ya bada dama bayan hawan sabuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari aka gano ma’aikata dubu hamsin na bogi dake karbar kudi da sunan gwamnatin tarayya wanda ake yiwa lakabi da (Ghost Workers).

Wannan rarar kudin da aka samu na ma’aikata dubu hamsin, su ne gwamnatin tarayya tayi amfani dasu inda ta debi sabbin ‘yan sanda dubu hamsin.

Treasurer Single Account (TSA): Sanusi Lamido Sunusi shi ya tsaya kai da fata wajen ganin gwamntain tarayya a wancan lokacin ta fara amfani da tsarin asusun bai daya.

Shima TSA ya kawowa gwamnatin tarayya damar samun rarar kudade, kuma daga nan ma’aikatu da makarantun gwamnatin tarayya, su ke biyan kudadensu kai tsaye zuwa ga asusun na bai daya ta hanyar amfani da Remita.

Labarai masu alaka:

Sarkin Kano ya bude masallacin juma’a na sabuwar jami’ar Bayero

Tilas a magance cin zarafin mata- Mai dakin Sarkin Kano.

Baya ga wadannan akwai tarin ayyukan jin kan al’umma na gine-gine da samar da ababan more rayuwa da CBN ta rikayi a ko ina a fadin kasar nan a lokacin shugabancin Sanusi Lamido Sanusi.

Sanusi Lamido ya samu lambobin yabo da dama daga ciki akwai ta Mujallar Banker Magazine dake birnin London wanda ta bashi kyautar gwarzon gwamnan banki a shekara ta 2010.

Har ila yau a shekara ta 2013 a yayin taron shekara na asusun bada lamuni na majalisar dinkin duniya (IMF) da aka gabatar a birnin Washington DC na kasar Amurka, an baiwa Sanusi Lamido lambar yabo ta Central Bank of the year, wadda a wannan lokaci shi ne karon sa na uku na samun wannan lambar yabo.

A zamanin sa na Gwamnan babban bankin kasa manoma sun amfana da shirye shirye

da dama yayin da kuma matasa suka sami ayyukan yi na dogaro da kai.

Karanta wadannan:

Tilas a magance cin zarafin mata- Mai dakin Sarkin Kano.

Sarkin Kano da Lamidon Adamawa sun gana da shugabannin Fulani don magance rikicin Fulani makiyaya

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!