Labarai
Al’amura sun koma dai-dai a kasuwar Singa bayan tashin Gobara

Al’amura sun fara komawa dai-dai a kasuwar sayar da kayan masarufi ta Singa da ke Kano, bayan tashin wata gobara da misalin ƙarfe 4:00 na Asuba, a kan titin Ado Bayero da ke cikin kasuwar.
Sakataren gamayyar ƙungiyoyin yan kasuwar ta Singa, Kwamared Ibrahim Nafi’u Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan a zantawarsa da wakilin Freedom Radio Abba Isah Yakasai, ta wayar Tarho.
Kwamared Ibrahim Nafi’u ya bayyana cewa babu asarar rai da aka samu, sai dai an yi asarar dukiya ta miliyoyin naira.
You must be logged in to post a comment Login