Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Allah ya yiwa sarkin tsaftar Kano Alhaji Ja’afaru Ahmad Gwarzo rasuwa

Published

on

Allah ya yiwa sarkin tsaftar Kano Alhaji Ja’afaru Ahmad Gwarzo rasuwa.

Guda daga cikin ƴaƴan sa mai suna Asma’u Ja’afaru ta tabbatar da rasuwar sa yayin zantawarta da Freedom Radio.

Ta ce, marigayin ya rasu a ƙasar Saudiyya jim kadan bayan yi masa aiki a zuciya.

Kafin rasuwar marigayin shi ne mai bai wa gwamnan Kano shawara kan harkokin tsaftar muhalli.

Ma’aikatar muhalli ta jihar Kano ta miƙa sakon ta’aziyyar ta ga gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da iyalan Marigayin.

Kwamishinan muhalli Dakta Kabiru Ibrahim ne ya miƙa saƙon ta’aziyyar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar Sunusi Abdullahi Ƙofar Nai’sa ya sanyawa hannu.

Saƙon ta’aziyyar na bayyana marigayi sarkin tsaftar a matsayin jajirtacce mai hidimtawa al’ummar sa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!