Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Almajirai: Gwamnonin Arewa ne suka hana tafiyar da tsarin inganta tsangayu

Published

on

Tsohon sakataren hukumar bada ilimi na bai daya Farfesa Ahmad Modibbo ya ce gwamnonin Arewa ne suka hana ruwa gudu a shirin inganta karatun Alkur’ani a jerin tsarin shirin manhajjar ilimin boko.

Tsohon shugaban ya bayyana haka ne a yayin wata lacca mai taken ‘Kafin hana tsarin almajirci a fadin Najeriya” Wanda cibiyar raya al’adu da bincike da ke jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria a jihar Kaduna suka gabatar a ranar asabar din da ta gabata.

Ya ce a lokacin mulkin tsohon shugaba Goodluck Jonathan , yayi yunkurin dauke almajirai a bisa manyan tituna , inda aka kashe makudan kudade wajen gina musu makarantun allo na zamani da zummar inganta harkar karatun tsangaya.

Amma abin takaici shine wadannan wurare sun zama tamkar kango da basu da amfani, sakamakon halin ko in kula da shugabannin yankin da aka gina suka yi makarantar.

Jaridar The Punch ta rawaito cewar, Modibbo ya ce gwamnonin Arewa sun bar makarantun ba tare da an sanya dalibai ba,inda aka bar makarantun ba tare da anyi amfanin komai da su ba,kamar yadda aka tsara a lokacin da aka kaddamar da shirin da gwamnatin tarayya ta fito da su.

Ya kara da cewa gwamnatocin basu ji dadin tsarin da gwamnatin tarayya ta fito da su ba,na shiga tsarin ilimin boko na dauke wadannan almajirai bisa kan manyan tituna , da asusun tara haraji na fannin ilimi suka tanada, domin kuwa a san ransu sun so a basu kudaden kwangilar maimakon dauko wasu daga waje domin gudanar da ayyukan.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!