Connect with us

Labarai

Kai tsaye: An dage cigaba da zaman majalisar Kano

Published

on

Shugaban majalisar dokoki ta Kano Abdul’aziz Garba Gafasa ya dage cigaba da zaman majalisa zuwa gobe Talata don fara tantance kunshin sunayen da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike wa majalisar da safiyar yau Litinin.

Wakilin mu na majalisar dokokin Kano Abdullahi Isah ya ruwaito cewa, majalisar ta kuma bukaci wadanda aka aike da sunayensu domin nadasu a matsayin kwamishinonin da su zo habar majalisar a gobe Talata domin fara tantancesu

Sunayen da gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya aike sun hada:

Murtala Sule Garo

Engr. Muazu Magaji

Barrister Ibrahim Muktar

Musa Iliyasu Kwankwaso

Dr. Kabiru Ibrahim Getso

Mohammed Garba

Nura Mohammed Dakadai

Shehu Na’Allah kura

Dr. Mohammed Tahir

Dr. Zahara’u Umar

Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa

Sadiq Aminu Wali

Mohammed Bappa Takai

Kabiru Ado Lakwaya

Dr. Mariya Mahmoud Bunkure

Ibrahim Ahmed Karaye

Muktar Ishaq Yakasai

Mahmoud Muhammad

Muhammad Sunusi Saidu

Barrister Lawan Abdullahi Musa

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje OFR ya aika da sunayen mutum 20 zuwa majalisar dokoki ta jiha domin tantance su da tabbatar da su a matsayin Kwamishinoni kuma yan majalisar zartarwa na Jihar Kano.

Kakakin Majalisa ne Abdu’aziz Garba Gafasa ya zaiyana sunayen a zaman majalisar da Safiya nan kuma ana sa ran fara tantancewar nan bada jimawa ba.

A dazun nan ne Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike da kunshin sunayen kwamishinonin da yake son nadawa don neman sahalewar su.

Daga cikin kunshin sunayen kawo yanzu da shugaban majalisar Abdula’aziz Garba Gafasa ya karantu cikin wasikar akwai tsohun kwamshinan Ayyuka na mussaman Musa Iliyasu Kwankwaso da tsohun kwamishinan kananan hukumomi  Murtala Sule Garo da Baba Impossible da Muntari Ishaq tsohun shugaban karamar hukumar Birni da Kewaye

 

Bayan da aka yi ta rade-raden da zarar ya dawo daga kasar Afrika ta Kudu zai nada kwamishinoni cikin kunshin Gwamnatin sa, kawo yanzu gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje bai sanar da ranar da zai yi wannan nadin ba.

A cikin karshen makonin da suka gabata ne aka yi ta ganin wasu kunshin sunayen tsofafi da sababin kwamishinoni, da wasu ke zargin sune kwamishinonin da Abdullahi Umar Ganduje zai nada.

Amma sai gashi sai yau Litinin ne 4 ga watan Nuwanba majalisar dokokin ta karbi wasikar kunshin sunayen kwamishinonin don neman sahalewar su.

Wakilin mu na majalisar dokoki ta jihar Kanop Abdullahi Isa  ya rawaito cewa na cigaba da karantu sauran sunayen a yayin zaman majalisar na yau Litinin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,893 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!