Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Al’ummar da ke kusa da madatsar ruwa ta kan Kangimi sun bukaci tallafi

Published

on

Al’ummar jihar Kaduna musamman wadanda suke zagaye da madatsar ruwa ta KANGIMI sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da su kawo musu dauki sakamakon zaftarewa da dam din ya fara yi don daukar mataki kafin ruwan ya balle.

Cikin al’umommin da suke kewaye da madatsar ruwan sun hadar da al’ummar kauyen Gobirawa, Ruhogi, Barkonu, Cikaji, Likoro, Unguwar Yamman Likoro, da kuma Girkawa duk cikin karamar hukumar Igabi.

Shugaban kungiyar masu suu na yankin karamar hukumar Malam Usman jikan Mudi shine ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai yace dam din ya fara nuna alamun ballewa tun shekarar da ta gabata sakamakon ruwan sama mai yawa da aka samu, inda yace tsawa ce tayi sanadiyyar tsagewar bangwayen dam din.

Malam Usman ya kuma kara da cewa tun lokacin ne kuma suka rubuta takardar korafi ga hukumar samar da ruwan sha ta jihar don daukar mataki amma yace har yanzu hukumar bata yi wani abu akai ba, inda yace hakan wasa ne da rayuwar al’umma duba da cewa zuwa yanzu ruwan ya fara ambaliya.

Ya kuma yi kira ga hukumar kare hakkin dan Adam da sauran kungiyoyin al’umma da su kawo musu dauki cikin gaggawa.

Da yake jawabi a madadin Gwamnatin jihar Kaduna mai baiwa Gwamnan jihar shawara kan harkokin yada labarai Sai’du Adamu ya tabbatar da cewa gwamnati zata yin duba kan al’amarin.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!