Connect with us

Kiwon Lafiya

Kungiyar manoma kashu ta kasa ce ta fitar da ‘yayan kashu na fiye da naira biliyan 140 kasashen waje

Published

on

Kungiyar manoma kashu ta kasa ta ce kasar nan ta samu naira biliyan dari da arba’in da hudu da miliyan dari bakwai wajen fitar da ‘yayan kashu zuwa kasar Vietnam da sauran kasashen duniya a shekarar da ta wuce.

Mai magana da yawun kungiyar Mr Sotonye Anga ne ya bayyana haka yayin zantawarsa da manema labarai a Lagos.

Ya ce tan dubu dari biyu da ashirin na ‘yayan kashu ne aka fitar da su zuwa kasashen Vietnam da Indiya da kuma China tsakanin watan Fabrairu zuwa Disamban shekarar da ta wuce.

A cewar sa cikin tan dubu dari biyu da ashirin na ‘yayan kashu din, sama da dubu dari da tamanin da daya an kai kasar Vietnam ne yayin da aka fitar da tan sama da dubu talatin da takwas zuwa kasashen Indiya da China.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,008 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!