Connect with us

Kiwon Lafiya

Al’ummar jihar Adamawa na dakon shugaba Buhari

Published

on

Rahotanni daga jihar Adamawa na cewa yanzu haka dai al’ummar Yola na dakon zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari gobe talata.

Ana sa ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da wasu manyan ayyuka da dama, tare da gabatar da jawabi yayin wani taro na musamman da gwamnatin jihar ta shirya kan yaki da cin hanci da rashawa.

A cewar rahotanni yanzu haka dai an kawata birnin Yola da fenti hadi da manyan alluna dake nuna maraba da zuwan shugaba Muhammadu Buhari.

A wata sanarwa da ya fitar, mataimakin gwamnan jihar Mista Martins Babale, wanda kuma shine shugaban kwamitin da ya shirya taron, yace gwamnatin jihar ta gama shiryawa tsaf domin karbar bakuncin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya bayyana cewa taron mai taken rawar da gwamnati take takawa, ana sa ran mukaddashin shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu da takwaran sa na hukumar yaki da cin hanci da rashawa ICPC farfesa Bolaji Owasanoye zasu gabatar da jawabi.Al

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!