Connect with us

Kiwon Lafiya

Gwamnatin tarayya ta ce zata haramata kamfanonin ketare hakar mai na ba da dadewa ba

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da dadewa ba za ta haramtawa kamfanonin hakar mai na kasashen ketare fitar da kafatanin danyan man da suka hako a kasar nan zuwa kasashen waje.

 

Haka zalika ta kuma ce za ta tursasawa kamfanonin Shell da Exxon Mobil da Chevron da sauran kamfanonin hakar mai na kasa da kasan da su gina sabbin matatun mai a kasar nan.

 

Ministan Albarkatun man fetur Dr. Ibe Kachikwu ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.

 

Ya ce komai ya gama kankama tare da fitar da jadawali da tsare-tsaren da ake bukata domin bukatar kamfanonin hakar man na ketare da ke ayyukan-su a kasar nan da su gina sabbin matatun mai.

 

A cewar ministan gina sabbin matatun man zai taimaka gaya wajen magance matsalar karanci mai na dindin-din a kasar nan.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,032 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!