Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Al’ummar wani kauye a Katsina sun kashe ‘yan bindiga 30

Published

on

Akalla ‘yan bindiga 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon kisan da al’ummar kauyen Majifa da ke yankin karamar hukumar Kankara da ke jihar Katsina su ka yi musu.

 

Rahotanni sun ce, al’ummar kauyen da suka hada da ‘yan kungiyar sintiri sun yi kofar rago ga ‘yan bindigar ne, kafin daga bisani suka afka musu wanda sanadiyar haka talatin daga cikinsu suka mutu.

 

Wani mazaunin kauyen na Majifa ya shaidawa jaridar Daily Trust cewa, lamarin ya faru ne a shekaran jiya litinin.

 

‘‘Da farko al’ummar kauyen sun samu labarin cewa, ‘yan bindigar suna shirin kai musu hari da dad-dare lamarin da ya sa su ka zauna cikin shiri, suka yi musu kofar rago, suka afka musu, sannan suka kashe talatin daga cikinsu’’ a cewar sa.

 

Rahotanni sun ce, ko a ranar lahadi da ta gabata, mazauna kauyen Magama da ke yankin karamar hukumar Jibia, sun dakile wani yunkurin harin da ‘yan bindigar su ka kai musu tare da kashe uku daga cikinsu.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!