Connect with us

Labaran Kano

Ambaliyar ruwa : Manoman shinkafa a Kano sun tafka asara

Published

on

Manoma a yankin karamar hukumar Garko anan jihar Kano, sun ce, ambaliyar ruwa ta yi sanadiyar lalata gonakin Shinkafa masu girman fadin kadada 89 a karamar hukumar Garko.

Sarkin noman Garko, Alhaji Sani Garba Garko ne ya bayyana hakan lokacin da ya ke zantawa da tawagar mataimakin gwamnan jihar Kano Alhaji Nasir Yusuf Gawuna wanda ya kai ziyarar jaje a yankin.

Nasiru Yusuf Gawuna wanda mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Bashir Idris Ungogo ya wakilta, ya nuna alhinin gwamnatin tare da jajanta musu da tabbatar musu da cewa zai kai rahoton abin da ya afku don daukar matakan da suka kamata.

Haka zalika, tawagar ta yi kira ga manoman da su jajirce wajen ci gaba da noman don samar da yalwataccen abinci ga kasa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!