Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

AMCON ta karbe kadarorin Buba Galadima

Published

on

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta umarci hukumar kwato kadarori ta kasa AMCON da ta karbe harkokin gudanarwar kamfanin Bedko wa fitaccen dan siyasar nan Alhaji Buba Galadima ya mallaka sakamakon tarin bashi da ake bin kamfanin wanda ya kai Naira miliyan dari tara.

Mai magan da yawun hukumar ta alkinta kadarorin Najeriya Jude Nwauzor ne ya bayyana haka a birnin tarayya Abuja.

Jude Nwauzor ya ce hukumar ta AMCON ta yi kokarin fito da wasu hanyoyi na ganin an magance matsalar tsakanin kamfanin na Alhaji Buba Galadima ba tare da anje kotu ba sai dai ya ci tura.

Mai Shariah AI Cikere ne ya bayar da umarnin ga hukumar alkinta kadarorin ta Najeriya na karbe kadarorin da Alhaji Buba Galadima ya mallaka.
Daga cikin kadarorin da aka karba akwai gida mai lamba goma sha biyar dake kan titin Addis Ababa a yankin Wuse dake birnin tarayya Abuja.

Sai kuma gida mai lamba hudu dake kan tiun bangui shima a birnin tarayyar dake Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!